Kungiyar Franklin Bulls ne zasu fara a wasan, Kai tsaye Payton Hughes ne ya karbi kwallon inda ya ke neman yadda zasu saka kwallon a ragar Kendry Rams da wuri-wuri, ya hango Tom Isaac Wanda ba ya cikin Yan baya a wasan, ya na ta lalube ne kawai yadda ya zama a gefe don satar numfashinsu, amma sai yan Bulls din su ka yi hanzarin dawowa don toshe wannan damar, abin sha'awa kariya ce Mai kyau haka nan abin burgewa a duk wannan lokaci Isaac na ta wannan bangare a kokarinsa na saka kwallo Mai maki uku, a jere amma Hakan Bai samu ba, zasu iya Kai hari kuwa, gagarumar dama ga Martins na Bulls ya saka kwallon a raga amma ba a bashi kwallon ba, ban taba ganin irin wannan ba, wasan kwallon kwando Mai matukar kayatarwa daga bangaren Rams...abin da mamaki